kasar Iran ya nakalto Sergey Lavrov yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa MIR tsarin biyan kudaden kasar Rasha na cikin gida ne wanda babban bankin kasar ta samar a shekara ta 2017, zai yi aiki tare da na kasar Iran ta yadda za’a iya amfani da tsarin a cikin kasashen biyu ba tare da wata matsala ba.
Ministan ya kammala da cewa tuni an shirya haduwar jami’an babban bakunan kasashen biyu don ganin hakan ya tabbata. Kafin haka dai Sergey Lavrov ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Husain Amir Abdullahiyan inda suka tattaunawa batituwa da dama daga cikin har da batun tsarin biyan kudaden.
Jaridar Rasha Today ta kasar Rasha ta bayyana cewa akwai gwamnatin kasar India ma tana tunanin amincewa da tsarin MIR na biyan kudade na kasar Rasha a kasar kamar da ana iya amfani da tsarin RuPay na kasar ta India a Rasha.
342/